ABNA24: Amurka ce ta haddasa dangantaka mai tsami tsakanin kasashen biyu na baya-bayan
- Kamfanin dillancin labaran “Javan” na kasar Iran ya nakalto jakadan kasar ta Sin a washinmgton ya na cewa gwamnatin kasarsa ba ta da anniyar bata dangantaka tsakanin kasashen biyu.
Ya kuma bukaci Amurka ta daina takalar kasar Sin don a maida huldar jakadanci tsakanin kasashen biyu kamar yadda take a da.
A makon da ya gabata ne gwamnatin Amurka ta rufe karamin Ofishin jakadancin Sin da ke jihar Texas tare da zargin ma’aikatan offishin da ayyukan leken asiri. Tare da bawa ma’aikatan sa’o’ii 72 na fice daga kasar Amurka.
A maida martani, gwamnatin kasar ta Sin ta bada umurnin rufe karamin ofishin jakadancin Amurka da ke birnin Changdoo.
Ya zuwa yanzu dai rigingimu tastanin kasashen biyu sun hada da yakin harkokin kasuwanci, takunkuman tattalin arziki kan kamfanonin kasar Sin wadanda suka hada da kamafanin sadarwan nan na Huawie, karfafa dangantaka da tsibirin Taiwan, halartar jiragen yakin Amurka a taken Sin da kuma tuhumar kasar ta Sin da samar da cutar korona.
342/