24 Yuli 2020 - 14:37
Barayin Daji A Jihar Katsina Sun Sake kashe Mutane Da Kuma Sace Dukiya

Barayin daji sun kashe mutane biyu da kuma wani malamin addini sannan kuma su ka yi awon gaba da dabbobi da kayan abinci a wani sabon hari da su ka kai a kauyen Kandawa da ke karamar hukumar Batsari a jahar katsina.

ABNA24: Jaridar Sahara reporters ta ambato wata majiya kauyen na Kandawa na cewa daga cikin wadanda aka kashe har da wani malamin addini.

Maharan da su ka shiga cikin garin akan babura sun dauki sa’o’i suna yin harbe-harbe ba tare da wani dauki daga jami’an tsaro ba.

A cikin watannin bayan nan dai hare-haren da barayin daji su ke kai wa a jahar katsina sun yawaita, inda a mafi yawancin lokuta su ke kashe mutane da sace dukiyarsu ta dabbobi.

342/