21 Yuli 2020 - 12:51
Fira Ministan Iraki Na Ziyarar Kwanaki Biyu A Iran

A wani lokaci yau Talata ne, ake sa ran fira ministan kasar Iraki, Mustafa al-Kadhimi, zai iso nan birnin Tehran, inda zai fara gudanar da wata ziyarar aiki ta kwanaki biyu.

ABNA24: Yayin ziyarar tasa, M. al-Kadhimi, zai gana da manyan jami’an kasar ta Iran, ciki har da shugaba Hassan Rohani, an kuma tsara zai gana da jagoran juyin juya halin musulinci na Iran din, Ayyatollah, Sayyid Ali Khamene’i.

Daga cikin wadanda ke mara masa baya a ziyarar tasa har da ministocin da suka hada dana harkokin waje, man feturm makamashi, kudi da tsaro da kuma kiwon lafiya, sai kuma wasu manyan ‘yan kasuwa, inda Bangarorin zasu tattauna kan batutuwa da dama da suka shafi kasashen biyu.

Ziyarar ta fira ministan Irakin, na zuwa ne bayan wacce ministan harkokin wajen kasar Iran, Muhammad Jawwad Zarif, ya kai a kasar ta Iraki, inda shi ma ya gana da manyan jami’an kasar ta dama.

342/