18 Yuli 2020 - 11:26
(EU), Amurka Na Barazana Da Takunkumi Domin Cimma Manufofinta

Kungiyar tarayyar turai ta yi tir da kakkausar murya da yayya gwamnatin Amurka ke yi wa kasashen duniya da bangarori daban daban barazana da sunan takunkumi domin cimma manufofinta na siyasa.

ABNA24: Da yake sanar da hakan babban jami’in harkokin diflomatsiyya na kungiyar ta EU, Josep Borrell, ya ce wannan ba abunda zai haifar da da mai ido ne ba.

Jami’in wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa ta kashin kansa yayin wani taron farfado da tattalin arziki turai, ya nuna jin takaicinsa kan yadda Amurka ke baraza da takunkumi ga masana’antu da kuma kaddarorin turai.

Ya kuma ce mun shaida yadda hakan ta faru ga kasashen Iran, Cuba da kuma kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC, sai kuma baya baya nan furicin da sakataren harkokin wajen Amurka ya yi na shirin kakaba takunkumi mai tsauri a shiri kasashen Rasha da Jamus na shinfida bututun iskar gas.

342/