14 Yuli 2020 - 14:12
Babban Bankin Najeiya Ya Dakatar Da Sayar Da Kudaden Waje Ga Masu Shigar Da Masara Cikin Kasar

Babban bankin kasar ta Najeriya, ya bayar da umarni ga dukkanin masu hada-hadar kudaden waje da su dakatar da amfani da tsarin sayar da kudaden waje ga masu shigar da masara cikin kasar, domin a bunkasa wacce ake nomawa a cikin gida.

(ABNA24.com) Takardar umarnin da aka aika wa masu hada-hadar kudaden waje a ranar Litinin din da ta gabata wacce kuma darakta na kasuwanci da musayar kudaden a babban bankin kasar, Dr. O.S Nnaji ya rattabawa hannu ta kunshi cewa;

“A karkashin kokarin da babban bankin Najeriya yake yi na kara samar da kayan masarufi a cikin gida, da kuma farfado da tattalin arziki, da kare rayuwar mutanen karakre da kuma samar da aikin yi, da aka rasa tun bayan bullar cutar covid-19, dukkanin masu hada-hadar kudaden waje masu lasisi an umarce su da su dakatar da amfani da tsarin bayar da kudin waje ga masu shigo da masara, nan take da gaggawa.”

342/