(ABNA24.com) Gidan Radiyon Faransa ya bayar da rahoton cewa, Farfesa Benedetta Allegranzi, jami’ar Hukumar Lafiya ta Duniya ce ta sanar da wannan sabon rahoto, inda ta ke cewa lalle sun tabbatar da wannan sabon bincike, saboda haka yana da muhimmanci mutane su fahimci wannan sabon matsayi domin kiyayewa.
Binciken da masana kimiya su 239 suka gudanar a duniya, ya nuna cewa cutar na iya tafiyar fiye da mita biyu, lokacin da wanda ya harbu da ita ya yi numfashi, ko kuma ya zubar da wani ruwa daga jikin sa.
Kafin wannan lokaci dai Hukumar ta ce ana yada wannan cutar ne sakamakon mu’amala tsakanin mai dauke da ita da kuma wanda baya dauke da ita, abin da yasa aka bukaci bayar da tazarar akalla mita biyu tsakanin jama’a wajen huldar yau da kullum.
Bisa alkalumman kididdiga na hukumar lafiya ta duniya, ya zuwa yanzu cutar corona ta kashe mutane dubu 546, da 629 a fadin duniya, bayan ta kama mutane miliyan 11 da dubu 950, 387, yayinda miliyan 6 da dubu 116 da 100 kuma suka warke daga cutar.
342/