(ABNA24.com) Wata sanarwa da ofishin shugaban kasar ya fitar, ta kuma isar da ta’aziya ga iyalai da makusantan wadanda suka rasa rayukansu a hadarurukan kwale kwalen guda biyu.
A ranar Lahadi, data gabata gwamman mutane ne suka rasa rayukansu a kifewar wani kwale kwake a kogin jihar Benue dake tsakiyar kasar.
Kafin hakan dama a ranar Juma’a data gabata mutum bakwai sun gami da ajalinsu a lamari irin wannan a garin Ikorodu dake kusa da jihar Lagos.
342/