5 Yuli 2020 - 12:05
Za A Dakatar Da Gwajin Wasu Magungunan COVID-19 - WHO

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce za ta dakatar da gwajin maganin hydroxychloroquine na jinyar masassarar cizon sauro da kuma hadin magungunan lapinavir/ritonavir na jinyar cutar HIV mai karya garkuwar jiki akan wadanda suka kamu da cutar COVID-19 ake kuma jinyarsu a asibiti, bayan da magungunan suka kasa rage adadin mace-macen da ake samu.

(ABNA24.com)  WHO, ta ce wannan matakin, wanda kwamitin da ke sa ido kan gwajin magunguna na kasa da kasa ya bada shawara a dauka, ba zai shafi sauran bincike-binciken da ake yi a bangarorin da ake amfani da magungunan kan marasa lafiyar da ba a kwantar a asibiti ba ko kuma a matsayin maganin kariya.

A daya bangare kuma Hukumar kula da lafiya ta MDD ta sanar da cewar, akwai yiwuwar samun sakamakon farko na gwajin maganin cutar COVID-19 nan da makonni biyu, a ta bakin babban Darektan WHO Tedros Ghebreyesus, saidai ba tabas akan lokacin da za’a iya wadatar da duniya baki daya ba da maganin, a cewar shugaban bangaren agajin gaggawa na hukumar Mike Ryan.

Kamfanin dilancin labaren AFP, ya ce zuwa jiya Asabar, adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a duniya ya zarce miliyan 11, inda ya kai miliyan 11, 145, 649 sannan, jimilar mutane 527 ,241 ne cutar ta yi ajalinsu a fadin duniya.

Kasar Amurka ce cutar ta fi yi wa illa, inda mutane 2, 818, 588 suka kamu, yayin da ta yi sanadin mutuwar 129 584.

342/