1 Yuli 2020 - 12:36
Iraqi:Dunkulewar Kasar Siriya Shi Ne Lamunin Zaman Lafiya A Yankin Asia Ta Kudu

Ministan harkokin wajen kasar Iraqi ya yi allawadai da takunkuman tattalin arziki wadanda gwamnatin kasar Amurka ta dorawa kasar Siriya.

(ABNA24.com)  Majiyar muryar Jumhuriyar Musulunci ta Iran ta nakalto Fawad Husain yana fadar haka a taron na 4 dangane da makomar kasar siriya wanda aka gudanar ta kafar sadarwa na hotunan bidiyo a birnin Brussel a jiya Talata.

Ministan harkokin wajen kasar na Iraqi ya kara da cewa dunkulewar kasar Siriya, yak i da kungiyoyin yan ta’adda a kasar da kuma kuma rashin shihsigi a cikin al-amuran kasar ta siriya su ne kadai hanyoyin warware matsalolin kasar .

Husain ya kara da cewa zaman lafiyar kasar Siriya dai-dai yake da zaman lafiya a kasar Iraqi, don sulalewar yan ta’adda daga kasar Siriya zuwa kasar Iraqi zai shafi zaman lafiya a kasar ta Iraqi.

Daga karshen Ministan ya bukaci kungiyar tarayyar Turai ta taimakawa ‘yan gudun hijirar kasar Siriya wadanda suke tarwatse a jasashen duniya daga cikin har da yan gudun hijiran kasar dubu 260 da suke cikin kasar Iraqi. Kungiyar tarayyar Turai ce take daukan nauyin tarurrukan na makomar kasar ta Siriya.

342/