(ABNA24.com) Masu zanga-zangar sun yi Allawadai da gwamnatin kasar Amurka dangane da yadda jami’an tsaron kasar suke murkushe masu zanga-zanga, wadanda suke neman adalci saboda kisan da aka yiwa wani bakar fata mai suna George Floyd fiye da wata guda da ya gabata a birnin Mineapolis daga arewacin kasar.
Kafin haka dai ‘yansanda a Amurka sun kashe bakaken fata da dama, ba tare da wani dalili na yin hakan ba, in banda launin fatar jikinsu.
Ya zuwa yanzu dai gwamnatin kasar ta Amurka ta ki amincea a gudanar da sauye-sauye a ayyukan ‘yan sandar kasar don kawo karshen wariyar da ake nunawa tsirarun kasar ta Amurka musamman bakaken fata ‘yan asalin nahiyar Afirka.
/129