28 Yuni 2020 - 06:51
An Zabi Nana Akufo-Addo A Matsayin Dan Takarar Shugaban Kasa Na Jam’iyyarsa

Jam’iyya mai mulki a kasar Ghana wato New Patriotic Party (NPP) ta zabi shugaban kasa mai ci Nana Akufo Addo a matsayin dan takarar jam’iyyar a zaben shugaban kasa wanda za’a gudanar a karshen wannan shekara.

(ABNA24.com)  Jam’iyya mai mulki a kasar Ghana wato New Patriotic Party (NPP) ta zabi shugaban kasa mai ci Nana Akufo Addo a matsayin dan takarar jam’iyyar a zaben shugaban kasa wanda za’a gudanar a karshen wannan shekara.

Wannan shine karo na ukku kenan da Addo yake kada tsohon shugaban kasar John Dramani Mahama a matsayin dan takarar jam’iyyar.

Nana Akufo-Addo, dan shekara 76 a duniya ya kada Mahama a zaben shugaban kasa na shekara ta 2016 tare da samun kashi 53.8% na kuri’un da aka kada.

A jiya Asabar ce Jam’iyyar ta NPP ta bada sanarwan cewa shugaba Akufo-Addo zai tsaya takarar shugabancin kasar a zaben da za’a gudanar a ranar 7 ga watan Decemba na wannan shekarar tare da Mahamudu Bawumia a matsayin mataimakin shugaban kasa.




/129