24 Yuni 2020 - 07:55
Iran Za Ta Aike Da Akwatinan Nadar Bayanan Tukin Jirgin Ukraine A Faransa

Ministan harkokin wajen kasar Iran, Muhammad Jawad Zarif, ya bayyana cewa kasarsa za ta aike da akwatinan nadar bayanan tukin jirgin fasinjan nan na Ukraine, da ya fado a kusa da birnin Tehran bayan harbo shi bisa kuskure zuwa kasar Faransa domin gudanar da bincike.

(ABNA24.com)  Ministan harkokin wajen kasar Iran, Muhammad Jawad Zarif, ya bayyana cewa kasarsa za ta aike da akwatinan nadar bayanan tukin jirgin fasinjan nan na Ukraine, da ya fado a kusa da birnin Tehran bayan harbo shi bisa kuskure zuwa kasar Faransa domin gudanar da bincike.

M. Zarif, ya bayyana hakan ne jiya Litini a wata hira ta wayar tarho da takwaransa na Canada, François-Philippe Champagne.

Iran, ta ce, dama ta shaida wa Ukraine cewa a shirye ta ke su tattauna kan duk batutuwan da suka shafi hatsarin ta fuskar shari’a, ciki har da biyan diyya ga iyalan wadanda suka rasu a hatsarin da kuma jirgin.

A watan Janairu ne jirgin fasinjan na Ukraine International Airlines, ya fado dauke da mutane 167, bayan harbo shi bisa kuskure sa’o’I kadan bayan harin martanin da Iran ta maida kan kisan Janar Shahid Qassem Solaimani a sansanonin sojin Amurka dake Iraki.


/129


/129