(ABNA24.com) Gwamnatin kasar Saudiya ta bada sanarwan cewa musulmi kimani dubu guda ne, sannan mazauna kasar ne kacal zasu gudanar da ayyukan hajjin bada.
Tashar talabijin ta Channel Tv a tarayyar Nigeriya ta nakalto ministan ayyukan Hajji na kasar Saudia Muhammad Benten yana fadar haka a yau Talata. Benten ya kuma kara da cewa gwamnatin kasar ta dauki wannan matakin ne don hana yaduwar cutar korona a cikin musulmi.
A shekarar da ta gabata dai musulmi kimani miliyon 2.5 ne suka gudanar da ayyukan hajji, miliyon 1.8 daga cikin su, sun shigo kasar ne daga kasashen waje. Amma bana, saboda bullar cutar korona a kasashen duniya da kuma ita saudiya, gudanar da aikin hajji kamar yadda aka saba ba zai yu ba, saboda kare mutane daga kamuwa da cutar ta Korona.
/129
24 Yuni 2020 - 07:21
Lambar labari: 1049752
Gwamnatin kasar Saudiya ta bada sanarwan cewa musulmi kimani dubu guda ne, sannan mazauna kasar ne kacal zasu gudanar da ayyukan hajjin bada.