(ABNA24.com) Ministan harkokin wajen kasar Siriya Walidul Mu’allim ya bayyana cewa “Dokokin Kaisar” wadanda gwamnatin Amurka ta dorawa kasar wata dama ce ga kasar ta tsayawa kan kafafunta a bangaren tattalin arziki, sannan ta kara dankon zumunci da kawayenya.
Tashar talabijin ta Al-Alam a nan Tehran ta nakalto Mu’allim yana fadar haka a wani taron ‘yan jarid da ya kira a yau Talata a birnin Damscus babban birnin kasar. Ya kuma kara da cewa gwamnatin kasar Siriya ta saba da mu’amala da irin wadannan takunkuman tattalin arziki, wadanda makiyan kasar suka dora mata, don haka da yardar All.. mutanen kasar Siriya zasu maida sabbin takunkuman tattalin arzikin da Amurka ta dorawa kasar, wadanda ake kira “Kanunu Kaisar” a matsayin wata dama ta dogaro da kansu da kuma wadanda suke goyon bayan kasar.
Daga karshen ministan ya bayyana cewa gwamnatin kasar Siriya za ta ci gaba da aiki da kawayenta, wadanda suka hada da Iran, Rasha da sauransu don rage tasirin da wadannan takunkuman zasu yi kan tattalin arzikin kasar, sannan za ta ci gaba da kasancewa tare da Falasdinawa a gwagwarmayansu na dawo da kasarsu da aka mamaye.
/129
24 Yuni 2020 - 07:20
Lambar labari: 1049749
Ministan harkokin wajen kasar Siriya Walidul Mu’allim ya bayyana cewa “Dokokin Kaisar” wadanda gwamnatin Amurka ta dorawa kasar wata dama ce ga kasar ta tsayawa kan kafafunta a bangaren tattalin arziki, sannan ta kara dankon zumunci da kawayenya.