(ABNA24.com) A sanarwar bayan taron kafar bidiyon da kasar Masar ta kira, ministocin harkoin wajen kasahen larabawan sun kuma bukaci a bude wata tattaunawa domin kawo karshen rikicin kasar.
Kungiyar ta kira taron ne kan halin da ake ciki a kasar Libiya, kan rikicin dake tsakanin gwamnatin hadin kan kasa ta Tripoli dake samun goyan bayan MDD, da kuma bangaren Khalifa Haftar dake da karfin iko a gabashin kasar.
Rikicin kasar ya kara tabarbarewa ne a ‘yan makwannin nan, bayan da gwamnatin Tripoli dake samun goyan bayan kasar Turkiyya ta matsa kaimi wajen neman kwace birnin Syrte daga hannun sojojin Haftar.
Wannan ne kuma ya sanya kasar Masar ta yi barazanar aikewa da sojojinta a kasar ta Libiya akan abunda ta danganta da keta jan layi idan rikicin ya iso iyakarta.
Gwamnatin Tripoli dai ta danganta barazanar ta Masar da takalar yaki.
Libiya dai ta fada cikin rudani ne tun bayan mutuwar tsohon shugaban kasar Mu’ammar Ghaddafi a cikin shekara 2011, bayan guguwar neman sauyin ta ‘yan kasar da kuma shigar sojojin kasashen yamma da suka hada da Faransa, Birtaniya da kuma Amurka a kasar, wanda ya taimaka wajen hambarar da gwamnatin ta Ghadaffin.
/129
24 Yuni 2020 - 07:20
Lambar labari: 1049746
Kungiyar kasashen larabawa ta butaci sojojin kasashen waje dasu gaggauta ficewa daga kasar Libiya.