23 Yuni 2020 - 03:24
Gwamnatin Kasar Iraqi Ta Jaddada Bukatar Kare Mutunci Da Kuma Kan Iyakokin Kasarta

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iraqi ta bada sanarwan cewa gwamnatin kasar ta bukaci tattaunawa na gwamnatin kasar Turkiyya dangane da samuwar mayakan kungiyar PKK a rewacin kasar da kuma tabbatar da cewa babu wata kasa wacce ta sake shiga kasar ba tare da imincewarta ba.

(ABNA24.com)  Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iraqi ta bada sanarwan cewa gwamnatin kasar ta bukaci tattaunawa na gwamnatin kasar Turkiyya dangane da samuwar mayakan kungiyar PKK a rewacin kasar da kuma tabbatar da cewa babu wata kasa wacce ta sake shiga kasar ba tare da imincewarta ba.

Kamfanin dillancin labaran Farsnews na kasar Iran ya nakalto Ahmad Assahaaf kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ya na fadar haka a yau Lahadi a birnin Bagdaza.

Assahaaf ya kara da cewa daga yanzun kasar Iraqi ba za ta kasance kasa wacce duk wanda ya so zai shigo, ba tare da sanar da ita ba.

A makon da ya gabata ne gwamnatin kasar Turkiyya ta tura sojojinta zuwa yankin kurdawa na arewacin kasar ta Iraqi don fatattakar mayakan PKK ba tare da sanar da gwamnatin kasar ta Iraqi ba.

Bayam haka ne dai gwamnatin kasar ta Iraqi ta kira jakadan turkiya a birnin Bagdaza inda ta mika masa takardan korafi mai tsanani kan abinda gwamnatin kasarsa ta aikata.

/129