21 Yuni 2020 - 08:19
Iran Ta Bayyana Matsayinta A Hukumance Kan Hukuncin Alkalan Hukumar IAEA

Gwamnatin kasar Iran ta sanar da matsayinta a hukunace kan hukuncin da alkalan hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya suka yanke dangane da shirin Iran na nukiliya.

(ABNA24.com) A cikin bayanin da ya fitar a yau, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Sayyid Abbas Musawi ya bayyana cewa, matakin na alkalan hukumar IAEA dangane da shirin Iran na siyasa ne, wanda kuma ya zo sakamakon matsin lamba ba kwarewa ba ko sanin makamar aiki.

Ya ce, sanin kowa ne kan cewa Iran ta bayar da hadin kai ga hukumar IAEA wajen gudanar da ayyukanta a cikin kasar fiye da kowace kasa ta duniya, kuma dukkanin rahotannin da hukumar ta fitar tun bayan cimma yarjejeniyar nukiliya a 2015 sun tabbatar da hakan, amma a halin yanzu sakamakon wasu dalilai na siyasa, hukumar ta canja matsayinta dangane da abin da ta rubuta.

Haka nan kuma Musawi ya bayyana takaicinsa yadda kasashen kungiyar tarayyar turai suka kasa zama kasashe masu ‘yancin siyasa, ta yadda a kowane lokaci suke bin son ran Amurka ido rufe ba tare da yin la’akari da maslaharsu ba.

Kamar yadda kuma ya jinjina wa sauran kasashen da suka yi watsi da hukuncin alkalan hukumar ta nukiliya, musamman gwamnatocin Rasha da China, wadanda suka yi watsi da rahoton hukumar dangane shirin Iran na nukiliya, tare da jaddada goyon bayansu ga kasar ta Iran.

Kamar yadda wasu daga cikin kasashe mambobi a hukumar da suka hada da Pakistan, Azarbaijan, Magnolia, India, Nijar, Pakistan, Afirka ta kudu, Thailand.


/129