21 Yuni 2020 - 08:19
​A Yau Ake Tunawa Da Ranar Shahadar Dr. Mustafa Chamran A Iran

A kowace shekara a kan gudanar da tarukan tunawa da zagayowar ranar shahadar Dr. Mustafa Chamrana kasar Iran, wanda ya yi shahada shekaru 39 da suka gabata a rana irin ta yau.

(ABNA24.com) Dr. Mustafa Chamran ya kasance ministan tsaron Iran na farko bayan juyin musulunci.

Chamran ya sami digirinsa na farko a Jami'ar Tehran, sannan ya tafi kasar Amurka don Karin karatu inda ya sami shahadar jkaratun digirin digirgir a fannin Engineer na wutar lantarki.

Daga baya ya zauna kasar Lebanon inda ya yi aiki da Imam Musa Sadr, a lokaci guda kuma yana daga cikin masu gwagwarmayar mulkin kama karya na sarki Shah a Iran.

Sai kuma bayan samun nasarar juyin juya halin Musulunci a Iran ya dawo gida inda aka nada shi Ministan tsaro na farko bayan samun nasar juyi, ya kuma taba zama dan majalisar dokokin kasar ta Iran.

A lokacin da gwamnatin Saddam Hussain ta kaddamar da yaki kan Iran tare da taimkaon Amurka da da kasashen turai da wasu kasashen larabawa, Dr. Mustafa Chamran a matsayinsa na ministan tsaro, ya tafi fagen fama da kansa, inda ya yi yaki kare kasarsa har shahada a rana irin ta yau.


/129