20 Yuni 2020 - 09:14
​ Mali : Zanga-zangar Neman Shugaba Keita, Ya Yi Murabus

A Mali, dubban 'yan kasar ne suka sake fitowa dafifi a Bamako babban birnin kasar, inda suka yi ta kiraye-kirayen kawo karshen mulkin Shugaban kasar Ibrahim Boubacar Keita.

(ABNA24.com)  A Mali, dubban 'yan kasar ne suka sake fitowa dafifi a Bamako babban birnin kasar, inda suka yi ta kiraye-kirayen kawo karshen mulkin Shugaban kasar Ibrahim Boubacar Keita.

Zanga zangar ta jiya Juma’a, ta biyo bayan makamanciyarta da aka yi makwanni biyu da suka gabata, ta neman shugaban kasar ya yi murabus saboda tabarbarewar al’amuran tsaro dake da nasaba da mayakan dake ikirari da sunan jihadi da kuma rikice rikicen kabilanci.

Yayin dai da wasu masu zanga-zangar ke kiran Shugaba Keita ya yi murabus, wasu kuwa kira suke da a kawo sauyi a bangaren siyasa na kasar da tattalin arziki da kuma kawo karshen cin hanci da rashawa.

Ko a ranar 5 ga watan nan an gudanar da irin wannan zanga zangar wacce ta samu halartar dubban mutane bisa kiran kawancen ‘yan adawa da wasu kungiyoyin farar hula da kuma fitaccen malamin addinin nan Mahmoud Dicko.

Bayanai daga kasar sun ce zanga zangar ta jiya ta samu halartar mutane da dama, fiye da ta makon da ya gabata, duk da tayin da shugaban kasar ya yi a farkon makon nan na kafa sabuwar gwamnati hadin kai wacce za ta kunshi har da ‘yan adawa.



/129