7 Yuni 2020 - 09:24
​Najeriya: Gwamnati Za Ta Rufe Wuraren Ibada Idan Ba A Kiyaye Ka’idojin Kiwon Lafiya Ba

Gwamnatin tarayyar najeriya ta yi barazanar rufe wuraren ibada a kasar, matukar dai jama’a ba su ka’idojin da aka gindaya ba, domin hana yaduwar cutar corona.

(ABNA24.com) Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha ne ya sanar da haka a daidai lokacin da jihohi ke bude masallatai da coci-coci.

Bayan matakan tsafta da bayar da tazara, an kuma umurci masu rauni, ciki har da ‘yan shekaru 55 zuwa sama da kuma masu ciwon suga, da ciwon zuciya ko kansa, da su ci gaba da yin ibada a gidajensu.

Mustapha, wanda kuma shi ne shugaban kwamitin da shugaba Buhari ya kafa domin yakar annobar corona a Najeriya, ya ce kwamitin zai ci gaba da wayar da kan jama’a game da ka’idojin bude wuraren ibada da sauran wuraren taruwar jama’a.

Ya ce; an mika wa gwamnatocin jihohi tsarin dokokin da Gwamnatin Tarayya ta tsara, kuma muna sa ran shugabannin addini za su yi na’am da su, dole ne a kiyaye su domin kauce wa yiwuwar jefa rayuwar jama’a cikin hadarin kamuwa da COVID-19, Muna kira da a yi taka-tsantsan a kowane lokaci.

Mustapha ya kuma kara da cewa wajibi ne a fadada wayar da kan jama’a zuwa kananan hukumomi, musamman wadanda ake ganin sun fi fuskantar barazanar kamuwa da cutar.

Jami’in ya jaddada muhimmancin yin amfani da shugabannin addini da sarakuna wurin wayar da kan jama’a game da annobar COVID 19.


/129