5 Yuni 2020 - 15:15
Rouhani:Abin Kunya Ne Yadda Shugaban Amurka Ya Fake Da Bible Wajen Halalta Kisan Amurkawa

Shugaban ƙasar Iran Dakta Hasan Rouhani yayi kakkausar da yadda shugaban Amurka Donald Trump yayi amfani da littafi mai tsarki na Bible wajen halalta ‘kisan gilla da sauran ayyukan take hakkokin bil’adama’ da yake yi a kan al’ummar Amurka masu zanga-zanga.

(ABNA24.com) Shugaba Rouhani ya bayyana hakan ne a yayin da yake magana kan zanga-zangar da al’ummar Amurka suke ci gaba da yi sakamakon kashe wani baƙin fata da wani ɗan sanda yayi inda ya ce: A halin yanzu muna ganin irin yadda ake amfani da ƙarfin wuce gona da iri wajen tarwatsa baƙaƙen fata da sauran al’ummar Amurka da suke nuna rashin amincewarsu da siyasar White House.

Shugaba Rouhani ya ce: Abin kunya ne yadda shugaban Amurka ya fake da littafin Bible wajen halalta umurnin da ya bayar na zubar da jinin Amurkawa da gudanar da sauran ayyukan take hakkoninsu da ake yi.

Shugaban na Iran ya ci gaba da cewa Littafin Bible dai wani littafi ne mai tsarki da ke kira zuwa da zaman lafiya da kuma tausayi. Ko shakka babu wannan aiki na Trump lamari ne da zai baƙanta ran dukkanin mabiya saukakkun addinai da kuma waɗanda suke girmama Annabi Isa al-Masihu da kuma littafin Bible.

A ranar Litinin ɗin da ta gabata ce Fadar White House ɗin ta fitar da wani hoton Trump yana riƙe da littafin Bible bayan da ‘yan sanda suka tarwatsa masu zanga-zanga a gaban fadar White House don ba shi damar zuwa wani coci da ke wajen.

342/