14 Mayu 2020 - 04:29
​Rasha Ta Ce Amurka Na Bata Lokacinta Kan Neman A Sabunta Takunkuman MDD A Kan Iran

Jakadan kasar Rasha a majalisar dinkin duniya Vassily Nebenzia ya bayyana cewa, abin da Amurka ke yi na neman kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya ya sabunta takunkumai kan Iran abin ban dariya ne.

(ABNA24.com) Jakadan kasar Rasha a majalisar dinkin duniya Vassily Nebenzia ya bayyana cewa, abin da Amurka ke yi na neman kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya ya sabunta takunkumai kan Iran abin ban dariya ne.

Tashar RT ta bayar da rahoton cewa, a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai jiya a babban zauren majalisar duniya a jiya, jakadan kasar Rasha a majalisar dinkin duniya Vassily Nebenzia, ya bayyana cewa, Amurka ba ta hurumin tsoma baki a cikin duk wani lamari da ya shafi yarjejeniyar nukilya da aka cimmawa tare da Iran, domin ba ta a cikin yarjejeniyar.

Ya ce a halin yanzu Amurka na ta kokarin ganin an warware abubuwan da kudirin majalisar dinkin duniya mai 2231 ya kunsa kan yarjejeniyar shirin Iran na nukiliya, wanda ya kunshi cewa a cikin watan Oktoban 2020 za a dauke wa Iran dukkanin takunkumai saye da sayar da makamai, inda Amurka ke kokarin ganin an sabunta takunkuman a kan Iran, jakadan na Rasha ya ce wannan abin ban dariya ne.

Ya kara da cewa, Amurka ba ta da wani hurumin da za ta iya sanya mambobin kwamitin tsaro su aiwatar da wannan manufa, domin kuwa ta sabawa doka da ka’ida wadda aka rattaba hannu a kanta.



/129