(ABNA24.com) Kasar Habasha, ta amsa cewa ita ce ta kakkabo wani jirgin Kenyan na dakon kayan agaji a kudu maso yammacin kasar Somaliya a farkon makon da ya gabata, amma bisa kuskure.
Hukumomin Habashar sun ce an samu kuskure ne wajen sadarwa tsakanin sojojin dake yankin wanda ya kunshi barikin sojin Bardale dake fuskantar barazanar hare haren mayakan al’shabab.
Habasha, ta ce jirgin ya nuna wasu halaye ne da ba’a yarda dasu ba, kuma yana shawagi a kasa kasa, kamar yana shirin hari, kamar yadda hukumomin kasar suka sanar a wata wasika da suka aike wa kungiyar tarayyar Afrika.
Jirgin na wani kamfani jiragen sama mai zaman kansa na (African Express Airways), ya fado ne ranar Litini data gabata dauke mutane 6 mambobin jirgin ‘yan asalin kasashen Kenya da kuma Somaliya, kuma dukkansu sun rasa rayukansu a hadarin jirgin.
Tun bayan hadarin ne kasashen Kenya da Somaliya ke binciken musababin faduwar jirgin wanda ke dakon kayan agajin jin kai dana asibiti domin yaki da cutar corona a Somalia.
/129
11 Mayu 2020 - 05:45
Lambar labari: 1035576
Kasar Habasha, ta amsa cewa ita ce ta kakkabo wani jirgin Kenyan na dakon kayan agaji a kudu maso yammacin kasar Somaliya a farkon makon da ya gabata, amma bisa kuskure.