(ABNA24.com) A Najeriya, adadin mutanen da suka harbu da cutar corona ya kai 3,912 kamar yadda hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta kasar ta sanar.
Adadin ya karu ne bayan samun karin wasu mutum 386 a jiya Juma'a.
Haka zalika, hukumar ta NCDC ta ce mutum 10 sun sake mutuwa a cikin sa'a 24, abin da ya sa yawan mutanen da suka mutu sakamakon cutar ta korona a Najeriya ya haura zuwa 117.
Har yanzu a Jihar Legas ne, cutar t afi kamari inda aka sake gano mutum 176 wanda kuma ya sanya yawan masu koronar a jihar ya kai 1,667.
Jihar Kano wacce ta ke a matsayi na biyu wajen masu fama da cutar, an samu karin mutum 65 a jiya Juma’a da suka harbu da cutar wanda ya sanya adadin mutanen da ke dauke da cutar a Kano ya kai 547, sai kuma 18 da cutar ta kashe.
Alkalumman baya baya nan su ne mafi yawa da aka taba samu a cikin sa’o’I 24 tun bayan bullar cutar a kasar.
/129
9 Mayu 2020 - 05:44
Lambar labari: 1034810
A Najeriya, adadin mutanen da suka harbu da cutar corona ya kai 3,912 kamar yadda hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta kasar ta sanar.