(ABNA24.com) Kamfanin dillancin labaran kasar Iran IRNA ya bayar da rahoton cewa, girgizar kasar ta auke ne tsakar dare wayewar garin yau Juma’a a yankin Damavand da ke tazarar kilo mita 58 daga birnin Tehran, fadar mulkin kasar.
Shugaban hukumar kula da ayyukan daukin gaggawa a kasar Iran Isma’il Najjar ya bayyana cewa, bayan aukuwar girgizar kasar wadda nauyinta ya kai daraja 5.1 a ma’aunin richter, wani mutum mai kimanin shekaru 60 ya rasa ransa a lokacin da yake kokarin gudu, sai kuma wasu 33 sun jikkata.
An ji motsin girgizar kasar a cikin birnin Tehran da ma wasu yankunan da suke gefen birnin.
Wasu daga cikin yankunan kasar Iran na a kan layukan girgizar kasa wadanda suka ratsa cikin wasu daga kasashen yankin gabas ta tsakiya da kuma kudanci da gabashin Asia.
/129
9 Mayu 2020 - 05:44
Lambar labari: 1034805
Da jijjifin safiyar yau Juma’a ne dai aka yi wata girgizar kasa a kusa da birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar mutum guda tare da jikkatar wasu 33.