3 Mayu 2020 - 04:59
Aljeriya : Ba Zamu Karbi Bashi Daga IMF Ba, Duk Halin Da Ake Ciki

Shugaba, Abdelmadjid Tebboune, na Aljeriya ya bayyana cewa kasarsa ba zata karbi bashi ba daga asusun IMF, ko bankin duniya, duk da barazanar rashin kudi da kasarsa ke fuskanta sakamakon annobar coronavirus da kuma faduwar farashin mai a duniya.

(ABNA24.com) Shugaba, Abdelmadjid Tebboune, na Aljeriya ya bayyana cewa kasarsa ba zata karbi bashi ba daga asusun IMF, ko bankin duniya, duk da barazanar rashin kudi da kasarsa ke fuskanta sakamakon annobar coronavirus da kuma faduwar farashin mai a duniya.

M. Tebboune, wanda ke bayana hakan a wata hira da ‘yan jarida ya danganta ciyo bashi da sabawa hurumin kasa.

Shugaban kasar ta Aljeriya, ya ce ya fi son ya ci bashi wajen ‘yan kasarsa maimakon ya nemi bashi ga asusun bada lamani na duniya, ko bankin duniya ko wani abu da ya yi kama da hakan.

Ya ce idan muka karbi bashi daga IMF, ko kuma bankuna kasa da kasa, to ba zamu taba magana akan al’ummar Palasdinu ba ko kuma ‘yan Saharaoui ba, wadanda a cewarsa abubuwa guda biyu ne masu matukar mahimmanci ga kasarsa Aljeriya.

Don haka a cewarsa karfinmu guda kan annobar Korona, shi ne kada mu ciyo bashin IMF.

Shugaban kasar ta Aljeriya ya kara da cewa akwai kasashe amminnan kasar da dama da suka yi masa tayin bashi, saidai bai amince ba har yanzu.




/129