(ABNA24.com) Dakarun Hashd Al-sha’abi na kasar Iraqi sun bayyana yadda suka sami nasarar dakile wani harin da ‘yan ta’adda na kungiyar Daesh suke so kaiwa a yankin Salahuddin na arewacin kasar.
Tashar talabijin ta Al-Alam a nan Tehran ta nakalto bayanin da dakarun suka fitar yana cewa, dakarun Hashd Al-sha’abi sun kashe ‘ya’yan kungiyar ‘yan ta’adda ta Daesh a garuruwan Balda da kuma Makeshefah a lardin Salahuddin da dama.
Bayanin ya kara da cewa dakarun sun rasa mayaka 10 da kuma wasu da suka ji rauni a fafatawar ta lardin salahuddin. Bayanin ya kara da cewa a halin yanzu wadanda suka ji rauni suna jinya a asbotocin kasar.
Har’ila yau bayanin ya ci gaba da cewa rundunar “Fawj Dajlah” ta rasa mayaka 9 da wadanda aka jiwa rauni 2. Sai kuma “rundunar Liwa, wacce ta rasa mayaka 41 a yankin “Tal-Zahab”.
/1298
3 Mayu 2020 - 04:59
Lambar labari: 1032650
Dakarun Hashd Al-sha’abi na kasar Iraqi sun bayyana yadda suka sami nasarar dakile wani harin da ‘yan ta’adda na kungiyar Daesh suke so kaiwa a yankin Salahuddin na arewacin kasar.