16 Afirilu 2020 - 04:59
Iran: IRGC Sun Kera Na’ura Mai Gane Cutar Corona Da Sauri

Dakarun juyin juya halin musulunci na Iran (IRGC) sun kaddamar da wata sabuwar na’ura wacce take iya gano cutar Corona Virus a cikin jikin mutane ko kuma a duk wani wuri wanda cutar take a cikinsa, a cikin dakikoki 5 biyar kacal.

(ABNA24.com) Dakarun juyin juya halin musulunci na Iran (IRGC) sun kaddamar da wata sabuwar na’ura wacce take iya gano cutar Corona Virus a cikin jikin mutane ko kuma a duk wani wuri wanda cutar take a cikinsa, a cikin dakikoki 5 biyar kacal.

Tashar talabijin ta Al-alam a nan Iran ta nakalto Manjo Janar Husain Salami babban kwamandan dakarun na “IRGC” yana cewa na’urar wacce ita ce ta farko a duniya, tana amfani da karfin maganadisun wanda cutar take fitarwa don gano inda take.

Salami ya kara da cewa na’urar wacce aka ba ta sunan “Musta’an” tana iya gano cutar corona a jikin mutane daga nisan mita 100 ba tare da an dauko jininsu ba.

Banda haka babban kwamandan na IRGC ya kara da cewa ana iya kara karfin wannan na’urar nan gaba don kara ingancinta daga kashi 80% da take da shi a halin hanzu zuwa sama.

Kafin haka dai an gwada wannan na’urar a asbitoci da kuma wurare da dama a cikin kasar, inda aka tabbatar da ingancin ayyukanta da kuma sakamakon da take bayarwa.



/129