(ABNA24.com) Turkiyan dai ta fara yin jigilar masu akidar Takfiriyyah daga kasar ta Syria zuwa Libya, tun bayan da majalisar dokokin kasar ta amince wa gwamnatin Ankara ta tura sojoji zuwa kasar ta Arewacin Afirka da ke fama da yakin basasa.
Wata kungiyar kare hakkin dan’adam ta ‘yan adawar kasar Syria, ta ambato wata majiya na cewa; A jiya Asabar ne Turkiyan ta aike da ‘yan ta’addar su 300 a karkashin rundunar Sultan Murad zuwa Libya
Kungiyar ta kara da cewa; An fara jigilar ‘yan ta’addar su 150 ne dai a cikin wasu motocin safa daga cikin garin Afrin na Syria zuwa kan iyakar Turkiya. Sai kuma wani ayarin na ‘yan ta’addar da aka yi jigilarsu daga Jabulus da al-Bab zuwa yankin Hawar Kellis na kan iyaka da Turkiya
Kungiyar ta masu adawa da gwamantin Damascuss wacce kuma take da matsuguni a birnin London, ta ce jumillar ‘yan takafiriyyah da Turkiya ta kai su zuwa Libya sun kai 5,050,kuma a halin yanzu da kawai wasu Karin 1,950 da Turkiyan take bai wa horon soja kafin su ma a tura su zuwa kasar ta Arewacin Afirka.
/129
13 Afirilu 2020 - 05:13
Lambar labari: 1025082
Turkiyan dai ta fara yin jigilar masu akidar Takfiriyyah daga kasar ta Syria zuwa Libya, tun bayan da majalisar dokokin kasar ta amince wa gwamnatin Ankara ta tura sojoji zuwa kasar ta Arewacin Afirka da ke fama da yakin basasa.