7 Afirilu 2020 - 08:33
An Samar Da Wani Sabon Kawancen Jam’iyyun Siyasa Na Yan Shi’a A Iraqi

Majiyar tashar talabijin ta Al-alam a nan Tehran ta bayyana cewa an samar da wani sabon kawance na jam’iyyun siyasa na ‘yan shia’a a wani taron da jam’iyyun suka gudanar a ranar Lahadi don zaben sabon firai minista a kasar.

(ABNA24.com) Majiyar tashar talabijin ta Al-alam a nan Tehran ta bayyana cewa an samar da wani sabon kawance na jam’iyyun siyasa na ‘yan shia’a a wani taron da jam’iyyun suka gudanar a ranar Lahadi don zaben sabon firai minista a kasar.

Majiyar ta kara da cewa sabuwar kawancen ya hadu kan kin amincewa da Adnan Zurfi wanda shugaban kasar ta Iraqi Barham Saleh ya ba shi damar kafa sabuwar gwamnati.

Majiyar ta kara da cewa sabon kawancen ya zabi sabbin ‘yan siyasa wadanda za su gabatar wa shugaban kasar don ya zabi wanda zai zama firai minista daga cikinsu.

Daga karshe ana sa ran sabon kawancen zai sami damar shawo kan sauran jam’iyyun siyasa don goyon bayan duk wani shugaban gwamnati wanda shugaban kasa zai zaba a cikin wadanda kawancen zai gabatar masa.

Tun bayan murabus din da firai minista rikon kwarya Adil Abdul Mahadi ya yi kimani watanni 3 da suka gabata, an gabatar da mutane biyu don kafa gwamnati amma sun kasa samun rinjaye a majalisar dokokin kasar.


/129