(ABNA24.com) Ma'aikatar tsaron Jamhuriyar Nijar ta sanar da cewa, sojojin kasar sun hallaka ‘yan ta’adda da yawansu ya kai 63 a yankin Tamalaoulaou dake lardin Abala a jihar Tillaberi dake yammacin kasar.
A sanarwar da ta fitar ma’aikatar ta ce, yayin da sojojin gwamnatin suke gudanar da aikin yaki da ta'addanci a yankin, a ranar 2 ga watan nan sojojin kasar sun yi arangama da ‘yan ta’addan, inda suka kashe 63 daga cikinsu.
Sojojin kasar sun kuma kwato babura da makamai masu yawa, sai dai kuma sojojin gwamnatin kasar 4 sun rasa rayukansu a fagen dagar.
Yankin Tillaberi dake yammancin kasar ta Nijar, na kusa ne da iyakar kasashen Mali da Burkina Faso, ya jima yana fuskatar hare hare daga ‘yan tada kayar baya dake da nasaba da kungiyar (IS) da wasu gungun kungiyoyin ta'addanci, lamarin da ya yi sanadin hasarar rayukan sojojin kasar ta Nijar da dama.
/129
5 Afirilu 2020 - 07:25
Lambar labari: 1022911
Ma'aikatar tsaron Jamhuriyar Nijar ta sanar da cewa, sojojin kasar sun hallaka ‘yan ta’adda da yawansu ya kai 63 a yankin Tamalaoulaou dake lardin Abala a jihar Tillaberi dake yammacin kasar.