1 Afirilu 2020 - 10:13
An Dage Babban Zaben Habasha, Saboda Barazanar Corona

Hukumar zabe a Habasha, ta sanar da dage babban zaben kasar da aka shirya yi a ranar 29 ga watan Agusta mai zuwa, saboda barazanar cutar corona.

(ABNA24.com) A sanarwar da ta fitar hukumar ta ce an dage zaben dama duk shirye shiryen da ake kansa har sai abunda hali ya yi saboda matsalar cutar ta corona.

Babu wani lokaci takamaimai da hukumar ta fitar domin gudanar da zaben, amma ta ce za ta fidda lokaci da zarar annobar ta corona ta kare.

An dai jima ana dakon zaben wanda ake ganin babban gimshiki ne ga gwamnatin firayi minista Abiy Ahmed, wanda ya lashe kyautar zaman lafiya ta nobel ta 2019.

A Habasha dai mutane 25 ne aka tabbatar sun kamu da cutar ta Covid-19, inda tuni hukumomin kasar suka sanar da daukar matakai ciki har da na hana tarurukan jama’a masu yawa da kuma tafiye tafiye ba dalili.

342