(ABNA24.com) Kafofin yada labarai daga Koriya ta Kudu, sun rawaito cewa Koriya ta arewa ta sake harba wani makamai mai linzami a safiyar yau Lahadi zuwa tekun Japon.
Bayanai sun ce wannan shi ne karo na hudu da Pyongyang ke harba makami mai linzami a cikin watan Maris din nan.
Tuni dai kasashen Japon da kuma Koriya ta Kudu, sukayi tir da sabon harbin makamin na koriya ta Arewa a daidai lokacin da duniya ta dukufa wajen yaki da cutar coronavirus.
Ko a ranar 21 ga watan nan Koriya ta arewa ta harba wasu makamai masu linzami guda biyu dake cin matsakaicin zango sakamakon rashin samun ci gaba a tattaunawarta da Amurka wacce ta shiga halin rashin tabas.
/129
30 Maris 2020 - 07:13
Lambar labari: 1021692
Kafofin yada labarai daga Koriya ta Kudu, sun rawaito cewa Koriya ta arewa ta sake harba wani makamai mai linzami a safiyar yau Lahadi zuwa tekun Japon.