22 Maris 2020 - 12:56
A Yau Ne Harkar Musulunci A Nigeria Ta Ke Bukin Tunawa Da Ranar Shahidai

Rahotanni sun bayyana cewa a yau Lahadi ne ake gudanar da bukcin tunawa da ranar shaidai da suka rasa rayukansu a harkar musulunci a Nigeria karakashin Jagorancin Shaikh Ibrahim Elzakzaki da gwamnati ke tsare da shi shekaru 4 ke nan tun bayan hari da sojoji suka kai gidansa da ke birnin zariya a shekara ta 2015

(ABNA24.com) Kiddidigar da gidauniyar kula da iyalan shaidai ta ta harkar musulunci a Nigeria ta fitar ya nuna cewa akwai kimanin ‘ya yan shahidai guda 2208 d take kula da su a halin yanzu, baya ga mataye da dama wadanda suka yi shahada a lokuta daban daban

Bayan Adduoi na bude taron za’a yi bayanai na tunawa da wadanda suka yi shahada, adadin mutanen ya karu ne sosai bayan harin da sojoji suka kai a gidan shehin malamin da yayi sanadiyar mutuwar dama da mutane 340 ,

Kimain shekarun 4 ke nan ana ci gaba da tsare jagoran harkar musulunci a Nigeria sheikh Ibrahim zakzaki duk da tarbarbarewar lafiyarsa, tare da mai dakinsa Mal Zeenatu , idan ana iya tunawa tuni wata kotu a birnin Abuja ta bada Umarni a saki shehin malamin da kuma biyansa diya , amma har yanzu gwamnati bata bi umar da kotu ta bayar na ta sake shi ba.

....
342