21 Maris 2020 - 10:46
Shamkhani: A Bara, Tsaron Kasar Iran Ya Fuskanci Mafi Girman Kalubale A Cikin Shekaru 40

Babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran, Ali Shamkhani ya bayyana cewa; A shekarar da ta gabata hukumar tsaron kasar Iran ta fuskanci manyan kalubale irin wadanda ba ta taba fuskantar irinsu ba a cikin shekaru arba’in da su ka gabata.

(ABNA24.com) Ali Shamkhani ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na twitter a jiya juma’a

Babban magatakardar majalisar koli ta tsaron kasar Iran din ya kara da cewa; Karfin da jamhuriyar musulunci ta Iran take da shi, yana kunshe ne a cikin salonta na iya kirkira.

Ali Shamkhani ya kuma kara da cewa; An shiga sabuwar shekarar hijira shamshiyya ne a daidai lokacin da hukumar tsaron kasar ta ke kara karfi.

.......

342