(ABNA24.com) Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iraki, ta kirayi jakadun kasashen Amurka da na Biritaniya, bayan jerin hare haren da jiragen yakin Amurka suka kai a kasar a cikin daren jiya Alhamis.
Tun da farko dai sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen Irakin, ta fitar ta yi tir da abunda ta danganta da tsokana ta Amurka, kan hare haren da ta kai kan sansanonin mayakan sa kai na “Hashdusshabi”.
Majiyoyi daga gwamnatin Iraki, sun ce an kai harin ne da misalin karfe 01:15 na dare jiya, kan sansanin mayakan da ke Jurf al-Nasr kilomita 60 daga birnin Bagadaza, da kuma Musayyib a cikin lardin Babil, kusa da hubbaren Imam Aliyu (a) da ke birnin Najaf da kuma wani harin a kan tsohon garin Alexandaria.
Ita ma dai ma’aikatar tsaron Amurka ta Pantagon ta tabbatar da kai wadannan hare-hare, wanda ta ce martani ne kan hare haren wasu rokoki da aka kai wanda suka kashe sojojin Amurka biyu da kuma na Biritaniya guda.
/129
14 Maris 2020 - 05:20
Lambar labari: 1017144
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iraki, ta kirayi jakadun kasashen Amurka da na Biritaniya, bayan jerin hare haren da jiragen yakin Amurka suka kai a kasar a cikin daren jiya Alhamis.