27 Faburairu 2020 - 06:08
An Samu Mutum Na Biyu Dauke Da Cutar Coronavirus A Afrika

Ministan kiwan lafiya na Aljeriya, ya tabbatar da kamuwar mutum na farko da cutar nan mai shafar numfashi ta coronavirus a kasar.

(ABNA24.com) Ministan kiwan lafiya na Aljeriya, ya tabbatar da kamuwar mutum na farko da cutar nan mai shafar numfashi ta coronavirus a kasar.

Ministan Abdel Rahman Ben Bouzid, wanda ke sanar da hakan a gidan talabijin din kasar, ya ce mutumin da ya kamu da cutar dan asalin kasar Italiya ne, wanda ya shigo kasar a ranar 17 ga watan nan, kuma tuni aka killace shi.

Wannan dai ya sanya Aljeriya ta zama kasa ta biyu a nahiyar Afrika inda aka samu mutimin farko dake dauke da cutar ta coronavirus.

A Kasar Masar ne dai aka fara samun mutum na farko da aka tabbatar yana dauke da cutar da ake kira covid-19 a nahiyar ta AFrika, saidai hukumomin kiwan lafiya na kasar sun ce mutumin ya warke amma yana ci gaba da jinya.



/129