(ABNA24.com) Ministan tsaron Iran, birigediya Janar Amir Hatami, ya bayyana cewa ayyukan tauraren dan adam na kasar basu da wata alaka da aikin soji.
Wannan dai na a matsayin maida martaki ga kasashen yamma a sahun gaba Amurka da Faransa, wadanda suka danganta ayyukan tauraren dan adam din Iran na baya bayan nan a matsayin wata hanya da ta neman karfafa makammai masu linzami na Iran.
A cewar birigediya Janar Hatami, na’urar harba tauraren dan adam ta (Simorgh), wacce ta harba tauraren dan adam na Zafar a ranar lahadi data gabata ba ta da wata alaka da aikin soji, hasali ma shiri ne na zaman lafiya.
Ministan ya kara da cewa tauraren dan adam za’a iya amfani da shi a aikin soji, amma na’urar cilla shi, bata shafi aikin soji ba, kuma kamar duk sauren kasashen da suka mallaki wannan fasaha, Iran ma na da yancin yin hakan, kuma zata ci gaba da wannan shirin.
A ranar Lahadi data gabata ce Iran, ta harba tauraren dan adam din ta na shida a sararin samaniya, saidai bai kai ba inda ake so ba domin fara aiki.
/129
13 Faburairu 2020 - 08:14
Lambar labari: 1010051
Ministan tsaron Iran, birigediya Janar Amir Hatami, ya bayyana cewa ayyukan tauraren dan adam na kasar basu da wata alaka da aikin soji.