13 Faburairu 2020 - 08:14
Salihi:Iran Ba Zata Mika Kai Ga Matsin Lamba Danagane Da Shirinta Na Nukliya Ba

Shugaban hukumar makamashin Nukliya ta kasar Iran, Ali Akbar Saliki ya bayyana cewa kasar Iran tana da kekkyawar dangantaka da hukumar IAEA mai kula da harkokin makamashin nukliya ta duniya. Amma ta bayyana cewa ba za ta amince ta mika kai ga bukatun wasu kasashen dangane da shirinta na makamashin Nukliya ba.

(ABNA24.com) Shugaban hukumar makamashin Nukliya ta kasar Iran, Ali Akbar Saliki ya bayyana cewa kasar Iran tana da kekkyawar dangantaka da hukumar IAEA mai kula da harkokin makamashin nukliya ta duniya. Amma ta bayyana cewa ba za ta amince ta mika kai ga bukatun wasu kasashen dangane da shirinta na makamashin Nukliya ba.

Salihi ya bayyana haka ne a lokacinda yake ganawa da sabon shugaban hukumar ta IAEA a Vienna. Amma ya ce kofar tattaunawa a bude take da kowa kan wannan shirin.

Daga karshe salihi ya bukaci sabon shugaban hukumar Ta IAEA Rafael Grossi, kada ya shigar da siyasa a cikin ayyukan hukumar.

A nashi bangaren shugaban hukumar ta IAEA, ya yabawa kasar Iran kan hadin kai da take bawa ma’aikatan hukumar, sannan ya yi fatan za ta ci gaba da bada hadin kai a lokacin jagorancinsa.

A shekara ta 2015 ne Iran ta cimma yarejejenta dangane da shirinta na makamashin Nukliya tare da manya-manyan kasashen duniya 5+1, amma sai shugaban kasar Amurka mai ci ya fice daga cikinta ya kuma dorawa kasar takunkuman tattalin arziki masu tsanani.

Har’ila yau sauran kasashen Turai uku wadanda suke rage a cikin yarjejeniyar sun kasa cika walkawalin da suka dauka a cikin yarjejeniyar saboda tsoron AMurka.


/129