Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: Bayan harin dabbanci da gwamnatin yahudawan sahyuniya suka kai a yammacin Khan Yunis da ke kudancin zirin Gaza a yau, shugaban sashen tiyata na "Nasser Medical Complex" ya sanar da kai shahidai fiye da 150 da waɗanda aka jikkata zuwa wannan asibitin.
