Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Lahadi

14 Janairu 2024

10:01:14
1429260

Za A Gudanar Da Taron Tunawa Da "Shahidai 'Yan Jaridun Gaza".

Tare da daukar nauyin Majalisar Ahlul Baiti (AS) da Kamfanin Dillancin Labarai na ABNA, za a gudanar da taron tunawa da Shahidai na Gaza.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: Wannan taro zai samu halartar Ayatullah Ramezani babban sakataren majalisar Ahlul-Bait (AS) ta duniya da wasu manyan mutane daga kasashen Palastinu da Yemen da Iraki da Turkiyya da Indonesia tare da halartar manajoji da masu fafutuka na kasa da kasa gobe a Litinin 15 ga watan Disamba a birnin Tehran – a dakin taron Majalisar Ahlul Baiti (AS) ta duniya.

Ya kamata a lura da cewa, gwamnatin yahudawan sahyoniya domin boye gaskiyar laifukan da take aikatawa a Gaza, ba wai kawai ta yada karya tare da taimakon kafofin yada labaran kasashen da ke da'awar kare hakkin bil'adama ba ne, a'a, har ma da kashe 'yan jarida a Gaza.

Bisa kididdigar da aka yi a baya-bayan nan sama da 'yan jarida 115 ne suka yi shahada a hare-haren da sojojin yahudawan sahyuniya suka kai a zirin Gaza.