Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Talata

2 Mayu 2023

13:55:39
1362010

An Ci Zarafi Wata Mata Mai Hijabi A Jamus

An ci zarafin wata Musulma mai hijabi a wata tashar jirgin karkashin kasa ta Berlin.

Kamfanin dillancin labaran Ahl al-Bait (A.S) ABNA ya bayar da rahoton cewa, a jiya litinin ne kafar yada labaran Jamus ta bayar da rahoton cewa, an ci zarafin wata musulma sanye da hijabi a wata tashar jirgin karkashin kasa ta Berlin.


Rundunar ‘yan sandan na kokarin zakulo wanda ake zargin ya furta kalaman batanci da kuma kokarin cire mata lullubi da karfi da yaji.


Lamarin dai shi ne na baya bayan nan a jerin hare-haren nuna kyama da kyamar baki da aka kai a babban birnin kasar ta Jamus wanda ya shafi baki ciki har da mata musulmi masu lullubi.


‘Yan sandan birnin Berlin sun tabbatar da cewa wata Musulma ‘yar shekara 20 ta samu kananan raunuka bayan da wani ya yi mata kalamai nuna kin jinin baki da karfin jiki a tashar jirgin kasa ta Rathaus Nukullen tare da yunkurin cire mata hijabi tare da jan gashinta.


A cewar rundunar ‘yan sandan, wanda ake zargin ya yi kalaman batanci na wariyar launin fata kafin ya gudu daga wurin, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano ko wanene maharin.


Kasar Jamus dai ta fuskanci karuwar wariyar launin fata da kyamar addinin Islama a cikin 'yan shekarun nan, sakamakon farfagandar kungiyoyi da jam'iyyu masu tsaurin ra'ayi da suka yi amfani da matsalar 'yan gudun hijira da kuma kokarin sanya fargabar 'yan cirani.


Hukumomi sun rubuta aƙalla laifuka 569 na kyamar Islama a cikin 2022, waɗanda suka haɗa da cin zarafi da na zahiri, wasiƙu na barazana, da kona masallatai.


.............................