18 Disamba 2022 - 19:52
Karatun Kur’ani Daga Ma’aikacin Hubaren Imam Hussain A Gaba Paparoma

An watsa faifan bidiyo na karatun "Osameh Al-Karbalai", fitaccen makaranci na hubbaren Hosseini a Karbala, a gaban Paparoma Francis, shugaban mabiya darikar Katolika na duniya, a yanar gizo.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na ABNA ya habarta cewa, Osama Karbalai daya daga cikin mashahuran makarantan kasar Iraki ne ya gabatar da wannan karatu a lokacin ziyarar da Paparoma ya kai birnin Ur na kasar Iraki mai tarihi a watan Maris din shekarar 2019.

A ziyarar da ya kai birnin Ur na tsohuwar kasar, Fafaroma Francis ya gudanar da addu'ar hadin gwiwa tsakanin addinai mai suna "Addu'ar 'ya'yan Ibrahim" a wurin da aka haife shi, sannan kuma ya saurari ayoyi daga kur'ani mai tsarki.

Karatun Usama Karbalai aya ta 40 da 41 a cikin suratu Ibrahim.



342/