Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Talata

5 Afirilu 2022

19:13:10
1245180

Turkiya Na Duba Yiwu war Daidaita Alaka Da Kasar Siriya

Majiyar labaran kasar Turkiya sun bayyana cewa gwamnatin kasar na duba yi yuwar fara tattaunawa da kasar Siriya , kuma ana saran tattaunawa za ta gina sabuwar dangantaka tsakanin kasashen guda biyu dake makwabtaka da juna.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Kasar Turkiya ta canza siyasar ta ne bayan rawar da ta taka abaya bayan nan musamman wajen ganin an kawo karshen yakin day a barke tsakanin kasashen Rasha da Turkiya wannan yasa ta ke ganin lokaci yayi da za’akawo karshen rikicin kasar Siriya

Har ila yau jaridar ta ci gaba da cewa dangantaka tsakanin Ankara da Damaskas ta fara inganta kuma zai kara bude wata sabuwar kofar dama ga kasar Turkiya musamman wajen warware matalar kungiyar kurdawa ta PKK mai neman ballewa daga kasar.

Ziyarar da shugaban kasar Siriya Bashar Asad ya kai Hadaddiyar daular larabawa a watan da ya gabata ya nuna cewa yana bukatar bullo da sabon salo da kuma samun goyon baya da zai taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a kasarsa.

sha’awar da kasar siriya take da shi na dawo da dangantakarta da kasar siriya yana zuwa ne baya da alakarta da wasu kasashen larabawa ta kara inganta a watannin baya bayan nan.

342/