ABNA24 : Wata sanarwa da sojojin suka fitar, ta bayyana cewa, karkashin sabon garanbawul din da suka yiwa majalisar zartarwar kasar, an nada sabbin ministoci 11 da za su kula da ma’aikatun kasar, yayin da aka tube mataimakan ministoci 24 daga mukamansu.
Sai dai kuma, ba a sauya babban alkali da alkalan kotun kolin kasar ba.
Wannan mataki na zuwa ne, bayan da ofishin shugaban kasar, ya ayyana dokar ta baci ta tsawon shekara guda, inda aka damkawa babban kwamandan manyan hafsoshin tsaron kasar, ikon kula da harkokin majalisa, da zartaswa da na shari’ar kasar.
Jiya da safe dai, sojojin suka tsare shugabannin kasar ta Myanmar, ciki har da shugabar gwamnati Aung San Suu Kyi, da shugaba U Win Myint, da ministoci da kananan ministocin yankuna, da wasu mambobin majalisar koli ta jam’iyyar NLD mai mulkin kasar.
342/