22 Agusta 2020 - 10:52
Kasashen Faransa, Birtaniya Da Jamus, Ba Za Su Goyi Bayan Amurka Ba Akan Aniyarta Ta Sake Kakaba Wa Iran Takunkumi

A wani bayani na hadin gwiwa da kasashen uku su ka fitar da shi, sun yi kira ga kwamitin tsaro na MDD da ya kaucewa daukar duk wani mataki wanda zai kara rabuwar kawuna, sannan kuma su ka jaddada cewa har yanzu suna aiki da yarjejeniyar Nukiliya.

ABNA24 : Har ila yau bayanin ya ce yin aiki da tattaunawa ne zai warware rashin fahimtar juna kamar yadda yake a karkashin yarjejniyar Nukiliyar ta Iran.

Bayanin na kasashen turai ya zo ne, bayan sabon yunkurin Amurka na sake dawo da dukkanin takunkuman da aka dauke wa Iran bisa yarjejeniyar Nukiliya da aka cimmawa shekaru biyar da su ka gabata.

Tun da fari, ministan harkokin wajen Amurka Mike Pempeo ya sanar da cewa; Amurka ba za ta bari Iran ta rika sayarwa da kasashen duniya tankokin yaki ba.

Wata majiyar diplomasiyya ta ce kasar Rasha ta bukaci da a yi taron MDD domin tattauna wannan batu na Iran.

342/