(ABNA24.com) Shugaban kasar China Xi Jinping ya jaddada cewa babu gudu babu ja da baya dangane da ci gaba da kara habbaka alaka tsakanin kasarsa da Iran.
Tashar alalam ta bayar da rahoton cewa, a cikin wani jawabinsa a jiya Asabar, shugaban kasar China Xi Jinping ya bayyana cewa, China da Iran suna yin aiki a bangarori daban-daban domin ci gaban al’ummominsu, kuam wannan alaka za ta ci gaba.
Ya ce a cikin ‘yan lokutan baya-bayan nan kasashen biyu sun dukufa ne wajen yin aiki tare domin yaki da cutar corona wadda ta addabi duniya baki daya.
Wadannan kalamai na shugaban kasar China dai na zuwa ne a daidai lokacin da Amurka ke yunkurin ganin ta yi amfani da majalisar dinkin duniya domin sabunta takunkuman hana saye da sayer da makamai a kan kasar, wanda zai kawo karshe a cikin watan Oktoba mai zuwa.
Kasashen rasha da China wadanda suke da kujerun din-din-din a kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya, sun sha alwashin yin fatali da wannan yunkuri na Amurka, matukar dai aka gabatar da batun agaban kwamitin tsaro.
/129
21 Yuni 2020 - 08:05
News ID: 1048581

Shugaban kasar China Xi Jinping ya jaddada cewa babu gudu babu ja da baya dangane da ci gaba da kara habbaka alaka tsakanin kasarsa da Iran.