(ABNA24.com) Ministan harkokin wagen kasar Iran Muhammad Jawad Zarif ya bayyana sabbin matakan da Amurka ta dauka na kara takurawa mutanen kasar dangane da shigo da abinci da magunguna daga kasashen waje ya kara tabbatar da ce takunkuman na ta’addanci ne.
Ministan ya bayyana haka ne a shafinsa na tweeter a jiya Lahadi, ya kuma kara da cewa maganar sakatarin harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya yi na cewa Iraniyawa suna da zabi na mika kai ga amurka don su ci a binci ko kuma yunwa ta kashesu.
A cikin sabbin matakan da Amurka da dauka don kara takurawa mutanen kasar Iran dai sun hada da tilastawa bankuna da cibiyoyin kodade a duniya su mikawa baitulmalin Amurka duk wata hulda da ta hadasu da Iran a karshen ko wani wata, don ma’aikatar kudaden ta tabbatar da cewa bankunan aiki da takunkuman da Amurka ta dorawa Iran.
/129
28 Oktoba 2019 - 08:05
News ID: 984763

Ministan harkokin wagen kasar Iran Muhammad Jawad Zarif ya bayyana sabbin matakan da Amurka ta dauka na kara takurawa mutanen kasar dangane da shigo da abinci da magunguna daga kasashen waje ya kara tabbatar da ce takunkuman na ta’addanci ne.