(ABNA24.com) Shugaban kasar Iran Dr. Hassan Rauhaniya bayyana cewa; Iran tana kokarin ganin an sami zaman lafiya ne mai dorewa ne a yankin gabas ta tsakiya.
Shugaban na kasar Iran ya kara da cewa; Shirin zaman lafiya na Hurmuz tana magana ne akan yadda kasashen yankin tekun pasha za su yi aiki tare domin tabbatar da zaman lafiya.
Shugaban kasar na Iran, wanda yake kan hanyarsa ta zuwa Amurka domin halartar taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya na shekara-shekara ya bayyana cewa; Taron da babban zauren Majalisar Dinkin Duniyar yake yi, yana a matsayin dam ace ga al’ummun duniya, musamman al’ummar Iran domin bayyana ra’ayoyinsu.
Bugu da kari Dr. Hassan Rauhani ya ce; Taron na MDD dama ce mai kyau, domin bayyana matakan rashin adalci da ake dauka akan al’ummar Iran, haka nan kuma wasu batutuwa da su ka shafi wannan yankin da kuma duniya baki daya.
/129
24 Satumba 2019 - 04:42
Lambar labari: 977611
Shugaban kasar Iran Dr. Hassan Rauhaniya bayyana cewa; Iran tana kokarin ganin an sami zaman lafiya ne mai dorewa ne a yankin gabas ta tsakiya.