(ABNA24.com) Majiyar sojojin siriya ta bayyana cewa sojojin zasu sake shiga yaki da yan ta’adda a yankin Idlib bayan da kungiyoyin yan ta’adda wadanda suke samun goyon bayan gwamnatin kasar Turkiya a lardin sun ki dakatar da bude wuta duk tare da dakatar da bude wuta wanda sojojin Siriya suka fara tun ranar daya ga watan Augustan da muke ciki.
Tashar talabijin ta Al-alam a nan Tehran ta bayyana cewa, a cikin bayanin da rundunar sojojin kasar ta Siriya ta fitar a jiya Litinin, ta bayyana cewa gwamnatin kasar Turkiya ta kasa aiwatar da alkawalin da ta dauka a taron suchi na gamsar da yan ta’addan da suke yakar gwamnatin siriya a lardin idlib na su dakatar da bude wuta kafin a sami mafita ta siyasa don warware rikicinsu da sojojin kasar.
Bayanin ya kara da cewa, yan ta’addan a lardin na Idlib sun cilla makaman roka a kan wurare da dama a kan lardin hama na kasar ta Siriya bayan da sojojin kasar suka dakatar da bude wuta don mutunta yerjejeniyar da aka cimma a taron suchi.
Daga karshe sojojin na siriya sun tabbatar da cewa zasu koma fagen daga har zuwa lokacinda zasu share yan ta’adda daga lardin na Idlib.
/129
6 Agusta 2019 - 07:11
Lambar labari: 967303
Majiyar sojojin siriya ta bayyana cewa sojojin zasu sake shiga yaki da yan ta’adda a yankin Idlib bayan da kungiyoyin yan ta’adda wadanda suke samun goyon bayan gwamnatin kasar Turkiya a...